in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi allah-wadai da kashe ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a Darfur
2013-10-14 10:28:28 cri

A ranar Lahadi 13 ga wata ne, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya yi allah-wadai da harin da aka kai yankin Darfur na kasar Sudan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ma'aikatan wanzar da zaman lafiya 'yan kasar Senegal guda 3, kana wani ma'aikaci da ke aiki a karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta hadin gwiwa tsakanin MDD da AU ya ji rauni.

A cikin wata sanarwa da kakakin Ban Ki-moon din ya bayar, ta ce, Mr. Ban ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan wadanda suka kwanta dama, kana ya bayyana juyayinsa matuka ga gwamnatin jamhuriyar kasar Senegal, lamarin da Mr. Ban ya ce, ba za a lamunta ba.

Wannan dai ba shi ne hari na farko da aka kai kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya ba, domin ko da a watan Yuli, wasu 'yan bindiga sun yi wa tawagar da ke aikin wanzar da zaman lafiya kwanton bauna a yankin na Darfur, inda suka halaka 'yan kasar Tanzaniya 7 da ke aikin kiyaye zaman lafiya, kana suka jikkata 17.

A shekarar 2007 ne kwamitin sulhu na MDD ya kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNAMID, wadda aka dora mata alhakin kare rayukan fararen hula da taimakawa wajen isar da taimakon jin kai a yankin Darfur, inda ake gwazba fata tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin da kawayensu masu dauke da makamai tun a shekara ta 2003, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane 300,000 tare da tilastawa kusan mutane miliyan 2 barin gidajensu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China