in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan gwamnatin Malawi sun yi zanga zanga ta kasa
2013-02-21 11:02:15 cri

A ranar Laraba ne dubban ma'aikatan gwamnatin kasar Malawi suka hau tituna a manyan biranen kasar guda uku suna zanga zangar lumana don nuna kin amincewarsu game da karancin albashi da kuma rashin kyakyawan yanayin aiki.

Tun ranar 11 ga watan Fabrairu ne ma'aikatan suka ki zuwa ofisoshinsu don tilasawa gwamnati ta kara masu albashi da kuma kyautata yanayin aiki.

Sakamkon wannan mataki, abubuwa sun tsaya cik a muhimman sassa na kasar kamar sashen kiwon lafiya, koyarwa da sufurin sama inda har ta kai ga aka soke sufurin jiragen sama daga ciki da ma wajen kasar a tashar jiragen saman.

Kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua ya ganewa idonsa masu zanga zangar cikin lumana tare da daruruwan jami'an tsaro dauke da makamai don tabbatar da lamarin ya tafi cikin tsanaki.

To amma kuma gwamnatin kasar ta Malawi ta bayyana matsayarta dangane da lamarin ranar Laraba da safe inda ta ce, tilas ma'aikatan su koma bakin aikinsu domin an yi aiki kan wani muhimmin karin albashi ga ma'aikatan gwamnatin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China