Wata majiya daga jihar Yobe a tarayyar Najeriya, ta bayar da rahoton cewa, wasu da ake zaton 'yan kungiyar nan ta Boko Haram, sun hallaka a kalla dalibai 47 a wata kwaleji koyon aikin gona dake garin Gujba mai nisan kilomita 50, kudu da garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.
Wani jami'in da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce, maharan sun abkawa dakin kwanan daliban ne a ranar Lahadi a lokacin da suke barci. A cewar wani jami'in kwalejin, dalibai da dama sun jikkata sanadiyar harin, yayin da aka garzaya da yawancin wadanda suka ji rauni zuwa asibitin jiha da ke garin Damuturu domin yi musu magani.
Ya ce, ana fatan gano yawancin gawawwakin, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da binciken yankin a ranar Lahadi don gano sauran wadanda suka mutu ko jikkata sanadiyar harin.
A sakon da ya aike da shafinsa na Facebook, senata Abubakar Bukola Saraki, ya tabbatar da cewa, mutane da dama sun mutu a lamarin, inda ya ce, 'Yau ba rana ba ce ta zargi ko nuna tsaya ga wani, amma rana ce ta daukar mataki don ganin an gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya, kana a baiwa hukumomin tsaro goyon baya don hana aukuwar hakan nan gaba.'
A jawabinsa, kakakin rundunar tsaro ta JTF Eli Lazarus, ya ce, a halin yanzu jami'an tsaro na kokarin bin sawun 'yan ta'addar, don ganin an damke su.
Idan ba a manta ba, a ranar 6 ga watan Yuli ma, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun hallaka a kalla dalibai 29 da kuma wani malami, a wani harin da suka kai wa wata makaranta a jihar ta Yobe. (Ibrahim)