in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COMESA za ta ware dalar Amurka miliyan 5 domin taimakawa kanana da matsakaitan masana'antu
2013-10-14 10:00:09 cri

Gamayyar kasuwancin kasashen kuriyar Afrika wato kudu maso gabashin nahiyar (COMESA) ta kafa wata gidauniya domin tallafawa kanana da matsakaitan kamfanoni (PME), a wani labarin da jaridar Times of Zambia ta rawaito a ranar Lahadi.

Sindiso Ngwenya, sakatare janar na kungiyar ya bayyana cewa, wannan asusun zai kebe kashi 25 cikin 100 na ribar da yake samu wajen ciyar da karfin kananan masana'antu a wannan shiyya. 'Muna bisa hanyar kaddamar da gidauniyar COMESA SME. Za a kaddamar da wannan gidauniyar a karshen wannan wata ko kuma a farkon wata mai kamawa. Haka kuma za mu soma da miliyan biyar na dalar Amurka, sannan kashi 25 cikin 100 na ribar da aka samu daga wannan asusu za su shiga wajen gina PME.' in ji mista Ngwenya.

Kungiyar COMESA na fatan ganin kananan masana'antu sun bunkasa, ta yadda za su zama manyan masana'antu domin samar da aikin yi ga jama'a.

Haka kuma jami'in ya kara da cewa, muhimman kalubale da wadannan kanana da matsakaitan masana'antu suke fuskanta a wannan shiyyar Afrika sun hada da rashin karfi da rashin jarin gudanar da harkokinsu.

Tare da kasashe 19 da kuma GDP da ya cimma dalar Amurka biliyan 485, kungiyar COMESA ta kasance babban gungun kasuwanci a nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China