Gwamnatin kasar Malawi ta sanar a ranar Alhamis cewa, shugaba Joyce Banda ba za ta halarci taro mai zuwa na kungiyar tarayyar Afrika da zai gudana daga ranar 9 zuwa 16 ga watan Juli a Addis Ababa a kasar Habasha ba.
Mataimakin shugaban kasar Khumbo Kachali, shi ne zai jagoranci tawagar kasar Malawi zuwa taron.
Ya kamata taron ya gudana A Lilongwe, babban birnin kasar ta Malawi ne kamar yadda aka tsara shirin a yayin taron karshe na kungiyar. A ranar 8 ga watan Yuni, gwamnatin kasar Malawi ta sanar da cewa, ba za ta iya shirya gudanar da taron ba, sabili da matsaloli game da shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bsshir da kotun kasa da kasa ta CPI ta ba da sammacin kama shi.
A ranar Talata, kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta tabbatar da cewa, taron zai gudana a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, ba a Lilongwe ba kamar yadda aka furta a baya.(Abdou Halilou)