in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun Nigeriya za ta yanke hukuncin karshe kan wanda ya kai hari a majami'a a Nuwamba
2013-10-08 11:01:12 cri

Babbar kotun kasar Nigeriya a ranar Litinin din nan ta bayyana cewa, za ta yanke hukuncin karshe a kan wani jigon 'dan kungiyar nan ta Boko Haram a wata mai zuwa.

Kotun za ta yanke hukunci a kan Kabiru Umar a ranar 7 ga watan Nuwamba bisa zargin laifukan ta'addanci da ake masa, in ji mai shari'a Adeniyi Ademola.

Hukumar leken asiri ta kasar a ranar 19 ga watan Afrilu ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya a kan hannu cikin harin da aka kai a mujami'ar St Theresa dake garin Madalla dake jihar Nijer ta kasar a ranar Krisimeti ta shekara ta 2011.

Laifukan da ake zargin Kabirun da aikatawa sun kasance karkashin laifukan ta'addancin da yaki da su na kasa na shekara ta 2011 kuma hukuncinsu zai fada a karkashin dokar.

Biyu daga cikin laifukan uku za su bukaci daurin rai da rai, sai dai wanda ake zargi ya musanta aikata su.

Da yake bayani a kotun, Sheriff Okoh, lauyan dake kare wanda ake zargin ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar da ake zargin Kabirun da shi saboda laifuka ukun da 'yan sanda da wassu masu gabatar da kara su biyu suka yi ba na gaskiya ba ne.

Ya ce, zargin da ake wa wanda yake karewa na cewar, shi 'dan kungiyar Boko Haram ne, bai kamata a yi amfani da shi ba saboda kundin tsarin mulkin kasar ba ta ce wanda ke cikinta ya zama mai laifi ba, sai bayan da aka kama wanda ake zargin, don haka wanda yake karewa bai yi laifi ba na kasancewa a kungiyar a wancan lokacin.

Babban mai gabatar da kara Chioma Nwegbu ta bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar Sheriff Okoh, tana mai cewa, wanda ake zargin ya amsa laifukansa duka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China