in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe tara da kogin Nijar ke ratsawa sun dauki niyyar samar da ruwan sha
2013-09-25 11:06:25 cri

Kwararru da hukumomin kasashen da suka hada da Benin, Burkina-Faso, Cote d'Ivoire, Kamaru, Guinee, Mali, Nijar, Chadi da Najeriya da kogin Nijar ke ratsawa sun bayyana niyyarsu a ranar Talata a birnin Abidjan kan samar da ruwan sha a cikin shiyyar.

Wadannan kwararru da suke taro a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire bisa tsarin zaman taron hukumar kogin Nijar (ABN) sun mai da hankali kan nagartattun ayyukan da aka gudanar da kuma wadanda za'a yi wajen samar da ruwan sha da kayayyakin tsabtace muhalli.

Darektan ofishin ma'aikatar kula da ruwa da daji ta kasar Cote d'Ivoire Aidara Gouesse ya yi kira ga mahalarta taron da su yi ayyukan da za su taimakawa wajen kyautata halin zaman rayuwar al'ummomin dake zaune a wannan shiyya ta nahiyar Afrika.

Haka kuma mista Gouesse ya yi kira da a cigaba da bunkasa hadin gwiwa daga dukkan fannoni domin kara ba da kulawa ga kogin Nijar. A cewersa, wannan haduwa tana da manufar kawo wani yunkuri na kula da albarkatun ruwa cikin hadin gwiwa da sa kaimi kan zuba jari kan ayyukan dake kawo cigaba.

Baya ga batun kyautata albarkatun ruwa, taron kuma zai mai da hankali kan wani shirin yaki da kwararar kasa. Kwararar kasa da kogin Nijar ke fuskanta, matsala ce dake hana cigaban noma, a cewar wani masani tare da bayyana cewa, wannan matsala ta kwararar kasa ta kara kamari a tsawon karni uku da suka gabata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China