in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Goodluck na Nigeria ya bukaci baiwa Afirka karin goyon baya
2013-09-25 09:51:08 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya yi kira ga kasashen duniya da su kara kaimi, wajen yin hadin gwiwa tare da baiwa kasashen Afirka karin goyon baya domin ciyar da nahiyar gaba.

Jonathan wanda ya gabatar da wannan bukata yayin da yake jawabi gaban mahalarta babban taron MDD dake gudana a hedkwatar majalissar dake birnin New York na kasar Amurka, ya ce, tsarin mulkin dimokaradiyya na ci gaba da habaka a dukkanin nahiyar Afirka, matakin da ya ce nasara ce babba ga nahiyar. Shugaban tarayyar Najeriyar ya kuma kara da cewa, a halin da ake ciki, nahiyar ta tashi daga matsayin mai neman tallafi kadai, zuwa nahiyar da ake damawa da ita a dukkanin lamurran da suka shafi kasashen duniya.

Da yake tsokaci kan kudurin cimma muradun karni kuwa, shugaban Najeriyar ya ce, ya zuwa shekarar 2015, akwai yiwuwar cimma manyan nasarorin da aka sanya a gaba, a lokaci guda kuma lokaci ne da ya dace a dada kaimi, wajen samar da managartan tsare-tsare bunkasa rayuwar bil'adama a nan gaba.

Babban taron MDDr da aka bude ranar Talata 24 ga watan nan na da burin samar da sabbin shirye-shiryen samar da ci gaba, da daidaito, da adalci tsakankanin kasashen duniya baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China