in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 38 ne suka mutu a wani harin ta'addancin da aka kai a kudu maso yammacin Pakistan
2013-08-09 15:38:47 cri

Kakofin watsa labarai da mahukuntan kasar Pakistan sun bayyana cewa, a kalla mutane 38 ne suka mutu, ciki har da manyan jami'an 'yan sanda yayin da sama da mutane 50 suka jikkata, sakamakon wani harin ta'addancin da aka kai a wajen da ake jana'iza ranar Alhamis da yamma a garin Quetta da ke kudu maso yammacin Pakistan.

Wani jami'in 'yan sanda mai suna Muhammad Tariq ya bayyana cewa, 'yan sanda 25 na daga cikin mutanen da suka mutu, yayin da aka kai gawawwakin fararen hula 6 wadanda suka hada da na yara zuwa asibitoci.

Kafofin watsa labaran sun ruwaito bayanan 'yan sandan na nuna cewa, an kashe manyan jami'an 'yan sanda wadanda suka hada da mataimakan sipeto janar na 'yan sanda mai kula da tsarin ayyukan 'yan sanda Fayyaz Sumbal yayin harin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China