A ranar Talata ne babban zauren MDD ya fara zamansa karo 68, a hedkwatar majalisar da ke birnin New York, inda ya mayar da hankalii wajen zayyana abubuwan da ake son aiwatarwa zuwa shekara ta 2015.
A jawabinsa na bude taron, shugaban babban zauren karo na 68, John William Ashe ya ce, a wannan karon, babban zauren zai mayar da hankali ne wajen gano abubuwan da ake son cimmawa ya zuwa shekara ta 2015, girman aikin, hadin gwiwar da ake bukata, don haka tilas a kara himma don ganin haka ta cimma ruwa.
Taken zaman na wannan karo, shi ne daura damara dangane da abubuwan da za su biyo bayan ajandar shekara ta 2015, wannan shi ne abin da ake son ginawa a kan irin ci gaban da manufofin muradun karni na MDGs suka cimma.
Ashe ya ce, sabuwar ajandar tana bukatar hadin gwiwa tsakanin dukkan bangarori, kuma za a yi kokarin shimfida matakan da za su kai ga samun ci gaba mai dorewa a duniya, wato shirin da zai mutunta kowa da kowa a wannan duniyar tamu.
Ya ce, yayin da duniya ke kokarin samun ci gaba mai dorewa bayan shekara ta 2015, zai gabatar da wasu manyan ayyuka da ke shafar mata, matasa, fararen hula, kare hakkin bil-adam, mutunta doka, hadin gwiwar Kudu ta Kudu, hadin gwiwar yankuna da shiyya-shiyya da samar da bayanan sadarwa na zamani don ci gaba. (Ibrahim)