in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kasar Somaliya na nuna fatan alheri kan taron Brussels
2013-09-16 12:54:54 cri

Mutanen kasar Somaliya na nuna fatan alheri sosai game da taron masu ba da taimako wajen sake gina kasarsu, da aka tsai da shiryawa a birnin Brussels na kasar Belgium ranar yau Litinin. Gwamnatin Somaliya da ma sauran mambobin gamayyar kasa da kasa za su tattauna wata sabuwar dangantaka mai taken 'New Deal' da za ta taimaka wajen kebe daruruwan miliyoyin dalar Amurka domin sake gina wannan kasa dake kahon Afrika. Haka zalika gwamnatin Somaliya na fatan ganin wadannan kasashe masu ba da tallafi za su kaddamar da wani sabon babi a cikin dangantaka tsakanin kasar Somaliya da gamayyar kasa da kasa kan wannan gidauniya ta sake gina kasar Somaliya. A bangaren al'ummomin Somaliya, cimma wata sabuwar yarjejeniyar sake gina Somaliya zai taimaka ga fadada sakamakon zaman lafiya da gwamnatin kasar ta samu. 'Ina fatan sabuwar yarjejeniya za ta kawo alfanu ga kasar Somaliya ta fuskar tattalin arziki, har ma a bangaren tsaro domin haka ya kasance wani babban cigaba ga gamayyar kasa da kasa.' in ji Moallim Ahmed, wani malamin wata makarantar dake birnin Mogadishu.

A ranar Lahadi, gwamnatin Somaliya ta bayyana cewa, shugaban kasar Hassan Sheikh Mouhamed zai halarci wannan taro a Brussels tare da wata babbar tawaga ta manyan jami'ai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China