in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta yi kira da a kawo karshen matsala tsakanin Isra'ila da Falasdinu
2013-09-17 10:45:53 cri

Kwamitin lura da harkokin diplomasiyya na majalissar dokokin kasar Afirka ta Kudu, ya yi kira ga kasashen duniya da su daukin dukkanin matakan da suka wajaba, domin kawo karshen wahalhalun da al'ummomin Falasdinu da na Isra'ila ke fuskanta.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar, wadda ke cewa, ya dace matuka a taimakawa bangarorin biyu, da managartan tsare-tsaren warware takaddamar dake ci gaba da wanzuwa a tsakaninsu.

Har ila yau kwamitin ya bayyana cewa, ya zama wajibi, a tabbatar da kafuwar kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci, wadda za ta kasance cikin aminci da makwafciyarta Isra'ila, bisa tsarin iyakokinsu na shekarun 1967.

Bugu da kari sanarwar ta bayyana goyon bayan kwamitin ga dukkanin matakan da kasar Afirka ta Kudun za ta dauka, na taimakawa wannan yunkuri, yana mai kira da a sanya daukacin kungiyoyi masu rajin kare hakkin 'dan adam dake kasar, cikin fafitikar kafuwar kasar Falasdinu, da ayyukan wanzar da zaman lafiya tsakanin Falasdinun da Isra'ila.

Tun a shekarar 1994, bayan kammalar mulkin nuna wariyar launin fata ne kasar ta Afirka ta Kudu, ke ci gaba da marawa al'ummar Falasdinu baya, a yunkurinsu na samun 'yancin kai, da tabbatar yanayin zaman lafiya da lumana tsakaninsu da gwamnatin kasar Isra'ila. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China