Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta sake nanata matukar bukatar da ake da ita, ta kaucewa daukar duk wani mataki da zai haddasa tashin hankali, ko barkewar tarzoma yayin da ma'aikatan sashen hakar ma'adanai ke gudanar da yajin aiki a sassan kasar.
Wannan kira da ya kasance irinsa na biyu cikin kwanaki goma, na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta tabbatar da hakin ma'aikatan na gudanar da yajin aiki bisa tanajin doka.
Mukaddashin kakakin fadar gwamnatin kasar Phumla Williams ce ta tabbatar da wannan batu, bayan kammala taron majalissar zartaswar kasar a birnin Pretoria, taron da ya mai da hankali kan tattauna batutuwan da suka shafi yajin aikin da 'yan kwadago ke ci gaba da gudanarwa yanzu haka a kasar.
Rahotanni daga Afirka ta Kudun dai sun tabbatar da cewa, yajin aikin da ma'aikatan hakar ma'adanai ke yi, da nufin tursasa kamfanonin su yi musu karin albashi, ya yi matukar tasiri ga sashen na hakar ma'adanai, da sashen gine-gine, da na makamashi, da kuma sashen sufurin kasar. Bugu da kari, ana ganin daukar wannan mataki zai yi matukar haifar da koma baya ga fannin tattalin arzikin kasar. (Saminu)