Rundunar hadin gwiwar jami'an tsaro a Maidugurin Najeriya ta ce, ta harbe wasu mutane 13 da take zargin 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne, yayin wata arangamar da rundunar ta yi da 'yan bindigar a unguwannin Bulabulin da Bayan. Dauki ba dadin da ya auku da sanyin safiyar ranar Talata 1 ga watan nan, a cewar mai magana da yawun rundunar Laftana Kanal Sagir Musa ya sabbaba rasuwar jami'in rundunar guda, tare da raunata wasu biyu.
Wata sanarwar da rundunar ta rabawa manema labaru ta bayyana cewa, baya ga 'yan bindigar 13 da suka rasa rayukansu, an samu damar karbe wasu makamai, ko da yake dai wasu daga cikin maharan sun arce yayin da a yanzu rundunar ke ci gaba da binciken gano su, da nufin amshe makaman dake hannunsu.(Saminu)