in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a hada kan iyakokin Nigeria da tauraron dan Adam domin inganta tsaro
2013-02-22 15:11:16 cri

Shugaban hukumar lura da shige da fice ta Nigeria Rilwan Musa, ya bayyana aniyar mahukuntan kasar, na samar da wasu naurorin tsaro da za a hada da tauraron dan Adam, wadanda za a rika amfani da su domin tantance shige da ficen al'umma dake bin iyakokin kasar.

Wannan dai sanarwa ta zo ne kwanaki 6, bayan sace wasu Turawan Faransa 'yan yawon bude ido a kasar Kamaru, aka kuma tisa keyar su zuwa Nigeria.

Shugaban hukamar ta lura da shige da fice ya kara da cewa, ya ziyarci jihohin Borno da Yobe, domin duba yanayin aikin da jami'ansa ke yi, da nufin tantance kalubalen da ake fuskanta, kafin daga bisani ya gabatarwa fadar shugaban kasa rahoto kan hakan, domin dai daukar matakan da suka dace.

Su dai wadannan jahohi biyu na da iyaka da kasashen Niger, da Kamaru, da kuma Chadi. Wanda kuma raunin tsaron iyakokin nasu, ke ba da dama ga bakin haure kwarara cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

Rilwan ya jaddada aniyar gwamnatin Nigeria, don gane da shirinta na samar da kayayyakin aiki, da tsare-tsare, da za su inganta sintiri a kan iyakokin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China