in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila shugaban Boko Haram ya mutu, in ji sojin Najeriya
2013-08-20 11:00:55 cri

Sojin Najeriya ya baiyana ranar Litinin cewa, kila an kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, sakamakon musayar wuta da sojojin Najeriya a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Ana kyautata zaton cewa, mai yiwuwa Shekau ya mutu ne a Amitchide, yankin kasar Kamaru dake da iyaka da Najeriya, wato lokacin da ake masa jinya sakamakon raunin bindiga da ya samu bayan arangama da dakaru kusa da sansaninsu dake dajin Sambisa, in ji wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar tsaro ta hadin gwiwa (JTF) Lt. Col. Sagir Musa ya bayar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayanin sirri da ayyukan maido da doka (ORO) na hukumar JTF ya samu, na nuna cewa, kila Shekau, wanda shi ne aka fi shakkarsa kuma ake nema ruwa a jallo, ya mutu.

Ya kara da cewa, ana tsammanin Shekau ya rasu tsakanin ranakun 25 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta.

Sojin ya baiyana cewa, shi ne ke da alhakin dasa bama bamai a wuraren ibada da na gwamnati har da shelkwatar 'yan sanda da kuma shelkwatar MDD dake Abuja.

A makon da ya wuce, cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ta samu, an ce, JTF ta yi ikirarin kashe mataimakin shugaban kungiyar Boko Haram a wani hari da dakaru suka kau da aukuwarsa.

Sanarwar ta nuna cewa, Momodu Bama mai inkiya da Abu Saad da cewa, shi ne mataimakin shugaban kungiyar. Kafin rasuwarsa a fadin JTF shi ne ke biye da Shekau a jerin shugabannin kungiyar Boko Haram. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China