in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kwadago a Afirka ta Kudu na shirin shiga yajin aiki
2013-09-04 10:02:04 cri

Kungiyar 'yan kwadago masu aikin hakar zinari a Afirka ta Kudu ta fidda wata sanarwa mai kunshe da barazanar shiga yajin aiki, muddin dai bukatarsu ta samun karin albashi ta ci tura.

Sanarwar shiga yajin aikin da kungiyar ta NUM ta fitar ranar Talata 3 ga wata, ta bayyana cewa, ma'aikata sama da 80,000 za su kauracewa ayyukansu, matakin da ko shakka babu zai yi matukar shafar kamfanoni, da ma sashen hakar ma'adanan kasar baki daya.

Tun daga shekarar da ta gabata, kamfanonin hakar ma'adanai a Afirka ta Kudu ke fuskantar matsalar yajin aiki a kai a kai daga ma'aikatansu, matakin da ke haddasa musu asarar tarin ribar da su kan samu.

A wannan karo ma dai kungiyar ta NUM ta lashi takobin tsunduma yajin aiki domin matsin lamba ga kamfanonin, har izuwa lokacin da za a amince da bukatarsu ta samun karin albashin da yawansa ya kai kimanin dalar Amurka 230 ga ma'aikatan dake aiki a doron kasa a ko wane wata, da kuma karin dala 300 ga ma'aikatan dake aiki a karkashin kasa

Tuni dai kungiyar 'yan kwadagon ta yi watsi da tayin karin kaso 6.5 bisa dari da kamfanonin suka gabatar gare su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China