in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Mugabe zai yi rantsuwar kama aiki a ranar Alhamis
2013-08-19 09:59:24 cri

Shugaba Robert Mugabe zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin zababben shugaban kasar Zimbabwe a karo na 6 ranar Alhamis mai zuwa, bayan da aka bayyana sunansa a matsayin mutumin da ya sake lashe babban zaben kasar da aka kada ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata.

Hukumar gudanar da zaben kasar ta Zimbabwe dai ta bayyana cewa, Mugabe, 'dan shekaru 89 da haihuwa ne ya lashe kuri'un da yawansu ya kai kaso 61 bisa dari, yayin da tsohon 'dan hamayyarsa, kuma firaminstan kasar Morgan Tsvangirai ke biye da kaso 34 bisa dari na jimillar kuri'un da al'ummar kasar suka kada.

Da fari dai sai da firaminista Tsvangirai ya shigar da kara kotu, yana kalubalantar sakamakon zaben da ya ce haramtacce ne, kuma cike yake da magudi da aringizon kuri'u, kafin daga bisani ya janye karar, bisa zargin cewa, ba za a yi masa adalci a shari'ar ba.

Sake darewar shugaba Mugabe bisa karagar mulkin kasar Zimbabwe a wannan karo, ya sanya shi kasancewa shugaban kasa mafi dadewa a dukkanin fadin nahiyar Afirka, wanda ya jagorantar kasar ta Zimbabwe tun daga lokacin da ta samu 'yancin kanta a shekarar 1980 kawo wannan lokaci.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, mafiya yawan shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar habaka kudancin Afirka ta SADC, da na ragowar sassan nahiyar Afirka, da ma na Latin Amurka, sun nuna amincewarsu da sakamakon zaben, sun kuma taya Mugabe murnar sake samun nasara. Sai dai a hannu guda, kasashen Amurka da Birtaniya sun bayyana shakkunsu kan sahihancin sakamakon zaben nasa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China