Babban alkalin kasar Godfrey Chidyausiku ne ya rantsar da Mugabe, kafin karfe 12 na rana agogon kasar, inda Mugabe ya ya alkwarin cewa, zai kare martaba da mutunta dokokin kasar, sannan ya yi fatan Allah ya taimake shi wajen sauke nauyin da ke wuyansa.
Ya kuma yi alkawarin cewa, zai kare kundin tsarin mulki da sauran dokokin kasar, kana zai karfafa dukkan abubuwan da za su taimawa wajen ciyar da kasar gaba tare da yin watsi da dukkan abubuwan da za su cutar da kasar Zimbabwe. (Ibrahim)