in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yajin aikin gama gari ya kama a kasar Afrika ta Kudu
2013-08-27 10:16:02 cri

A kasar Afrika ta Kudu ranar Litinin 26 ga wata, ma'aikata fiye da 140,000 na masana'antun kere-kere suka ajiye kayayyakin aikinsu domin neman karin kudin albashi a wata sabuwar yajin aiki na gama gari da yanzu haka ake yi a lokacin da kasar ke kokarin farfadowa daga sakamakon yajin aikin gama gari na shekarar bara da kungiyar kwadago ta kira.

Su dai wadannan ma'aikata yanzu za su bi sahun fiye da sauran ma'aikata 30,000 da suka rigaya suka fara yajin aikin mako daya da ya gabata.

Haka kuma a ranar Litinin din, daruruwan ma'aikatan filayen saukan jiragen sama su ma sun shiga yajin aikin, abin da ya kawo jinkiri a babban filin jiragen sama na kasa da kasa a Johannesburg, ganin shi ne kuma ranar da kungiyar ma'aikatan hako ma'adinai suka tsai da domin fara nasu yajin aikin, abin da ya sa gwamnati ta fitar da takardar gargadin cewa, duk wanda ya karya dokar kasar, to zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Sai dai duk da hakan, akwai rahotannin da suka nuna cewa, an samu tashin hankali a wani ma'aikatar kere-kere a birnin Johannesburg inda ma'aikatan suke yajin aiki, kuma wadansu da ba'a san ko su wane ne ba suka kai hari ta hanyar sara a kan mutane 7, ita dai uwar kungiyar ta yi tir ga aukuwar hakan tana mai cewa, in dai har 'ya'yanta ne suka aikata hakan, to za su fuskanci hukunci.

Kasar Afrika ta Kudu da yanzu haka take cikin yanayin yajin aiki, lokacin da ma'aikata da masu daukan aikin ke kokarin sabunta yarjejeniyar aikinsu, ta shawarci ma'aikata da su shiga tattaunawa mai ma'ana tsakanin su da shugabannin ma'aikatarsu domin cimma daidaito cikin hanzari. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China