Mahukunta sun tabbatar da cewa, mahakar platinum dake Lonmin a Marikana dake yankin arewa maso yammacin kasar Afirka ta kudu wacce ta sha fama da yajin aikin ma'aikata, a wannan karo ma ma'aikatan sun sake komawa yajin aiki ranar Talata.
Ma'aikata dake yajin aikin sun kai dubu 6 inda a wannan karo abin da suke bukata shi ne a rufe ofishin kungiyar ma'aikatan hako ma'adinai ta kasa NUM,saboda kungiyar ba ta da wani tasiri wajen kare hakkin ma'aikatan.
Kungiyoyin biyu wato na ma'aikatan hako ma'adinai ta kasa NUM da kungiyar ma'aikatan hako ma'adinai da gine-gine AMCU su na gaba da juna dangane da zama muhimmiyar jagora ga ma'aikatan. Wannan gaba tsakanin kungiyoyin biyu a lokuta da dama tana haifar da tashin hankali.
Mahakar ma'adinai ta Lonmin ita ce mafi girma ta uku a duniya da ake hako platinum, kuma a can ne aka sha fama da yajin aiki da ya bazu a shekarar bara.
A wata arangama da 'yan sanda a watan Agusta, ma'aikata masu hako ma'adinai a kalla 34 ne aka kashe a yajin aiki da ake ganin cewa, shi ne mafi muni tun bayan karshen mulkin wariyar launin fata.
Wannan bukata na kungiyar AMCU na cewar a rufe ofishin kungiyar NUM bai samu karbuwa a gun mahukuntan kamfanin ba.
Mai magana da yawun kamfanin, Mokoena ya bayyana cewa, matsayarsu dangane da wannan gardama shi ne abin da ke kunshe a yarjejeniyar da aka kulla ta zaman lafiya cewa, kungiyoyin biyu su ci gaba da wanzuwa tare.(Lami)