Rahotanni daga jihar Borno, dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga da ake zaton magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram ne, sun hallaka mutane a kalla 13, sakamakon wasu hare-hare da suka kai wasu yankunan jihar ta Borno.
Wata majiya daga rundunar tsaron jihar ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, maharan sun kaiwa kauyen Gamboru-Ngala harin ramuwar gayya da sanyin safiyar ranar Laraba ne, sakamakon kame wani 'dan uwansu da samarin kauyen masu aikin sa kai suka yi cikin makon da ya gabata.
Wadanda suka ganewa idanunsu aukuwar harin na ranar Laraba, sun ce, 'yan bindigar sun bude wuta cikin wani gida, lamarin da nan take ya sabbaba rasuwar mutane 4, tare da jikkata wasu mutane 8. Garin na Gamboru-Ngala wanda daya ne daga sansanin kungiyar ta Boko Haram, na da nisan kilomita 135 daga gabashin birnin Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno.
Baya ga harin na Gamboru-Ngala, rahotanni sun tabbatar da kai farmaki kan ofishin 'yan sanda dake garin Gwoza, da misalin karfe 8 na safiyar ranar ta Laraba. An ce, 'yan sanda 2 sun rasu, an kuma harbe mahara 7, yayin da 'yan bindigar ke dauki ba dadi da jami'an rundunar hadin gwiwar yankin. (Saminu)