Kwamishinan 'yan sandar jihar Edo dake kudu maso gabashin kasar Nigeriya Folunso Adebanjo a ranar Lahadin nan ya ce, rundunar za ta kubutar da wani sanannen lauya Mike Ozekhome da direbansa wanda aka yi garkuwa da shi.
Mr. Adebanjo kamar yadda ya sheda ma manema labarai a Benin, babban birnin jihar, duk da dai bai bayyana matakan da za'a dauka na ganin hakan ba, yana mai cewa, wannan wani sha'ani ne da ya shafi tsaro, amma sun sha alwashi ganin hakan ya tabbata.
Kwamishinan 'yan sanda Adebanjo ya sheida ma manema labarai cewa, a lokacin kokarin kubatar da shi tun da farko an yi musayar wuta an kashe mataimakin sufritanda na 'yan sanda, sepeto da wassu jami'an guda biyu.
Shi dai wannan lauya Mr. Ozekhome wani sanannen mai fafutukar kwatar 'yancin dan Adam ne ya yi kaurin suna wajen nuna kiyayyarsa ga ayyukan da ake aikatawa a gwamnati na zamba da sama da fadi da dukiyar al'umma kuma da shi da direbansa ne, wadansu mutane da ba'a san su ba suka sace su a ranar Jumm'a a karamar hukumar Ehor dake kan hanyar Benin zuwa Auchi.
A kwanakin baya ne dai majalissar dokokin jihar ta zartar da doka duk a kan wadanda aka kama da laifin sace mutane da yin garkuwa da su wanda hukuncin kisa ya hau kansu, sannan wadanda suka kwatanta niyyar satar mutanen kuma hukuncin rai da rai za'a yanke masu. (Fatimah)