in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta bukaci a daidaito a bangaren hako ma'adinai yayin yajin aiki
2013-08-28 10:11:10 cri

Mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu Kgalema Motlanthe a ranar Talatar nan ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su tabbatar da daidaito a bangaren hako ma'adinai a wannan lokaci da yajin aikin ma'aikata ke kara bazuwa.

Mr. Motlanthe wanda yake magana wajen taro karo na biyu na manyan masu ruwa da tsaki a bangaren ma'adinai wato 'Mining Lekgothan' a birnin Johannesburg ya ce, bangaren ma'adinai yana da muhimmanci sosai a wajen mayar da kasar wata ta zamani, domin ko a wannan rana ana cigaba da samar da wani abin tarihin kasar ne wanda zai daidaita kasar yadda ake son ta zama a nan gaba.

Ya lura cewa, a yadda ake da ma'aikata a wannan bangaren sama da 500,000, wannan bangare yana dauke da nauyin kashi 6 a cikin 100 na ma'aunin GDP kuma yana samar da kashi 60 a cikin 100 na kudin shiga da ake samu daga fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje na kasar baki daya, don haka ana ganin shi a wata kafar samar da kudin shiga mai muhimmancin gaske.

To sai dai wannan bangaren yana fuskantar barazana sakamakon gaggarumin yajin aikin da kungiyar kwadago ta kira a bara.

Kungiyar ma'aikatan hako ma'adinai a ranar Litinin din nan ta yi ikirarin cewar, kusan 'ya'yanta 90,000 ne suke yajin aiki don nuna bukatarsu na son karin kashi 13 a cikin 100 na albashinsu a wannan shekarar.

Ana dai ganin cewa, matsalolin bangaren hako ma'adinai ya faru ne sakamakon dadewar da aka yi da wassu tsarin kula da wannan wuri, da yadda ake tafiyar da ayyukan a wajen, da ma durkushewar tattalin arziki na duniya baki daya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China