in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi kiran ba da kujerun din-din-din ga Afirka a kwamitin sulhun MDD
2013-08-13 09:56:33 cri

A ranar Litinin, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya yi sauyi da kuma shigar da Afirka cikin kwamitin da akalla kujeru biyu.

Ministar dangantaka da hadin gwiwa na kasa da kasa ta kasar Maite Nkoana Mabashane ita ce ta yi wannan kira bayan karbar bakuncin shugaban babban taro na 67 na MDD Vuk Jeremic, a birnin Pretoria, hedkwatar harkokin gudanarwa na kasar.

Ta ci gaba da cewa, sun amince tare da sauran kasashe mambobin kungiyar AU guda 54 cewa, ba zai yiwu a samu sauyi ba muddin aka ci gaba da nuna halin ko oho da wariya ga wadannan kasashe 54 na yankin dake da muhimmanci.

Ta ce, matsaya guda da suka dage kai shi ne ba za'a samu wani sauyi ba, in ba tare da su ba domin kashi 70 cikin dari na batutuwa da ake tattaunawa a kwamitin wadanda suka shafe su ne.

A halin yanzu dai, nahiyar mai kasashe 54 na da wakilai wadanda ba na din-din-din ba a kwamitin guda uku, amma ba ta da ikon hawa kujerar ta ki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Afirka ta Kudu, Bua, ya yi nuni ranar Litini cewa, wannan kira da ministar ta yi ya zo ne daidai lokaci da ake muhawara kan cewar, ya kamata a baiwa Afirka kujerar din-din-din a kwamitin sulhu na MDD. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China