in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta karkato ga kasashen Afirka domin samo man fetur
2013-08-22 10:10:53 cri

A ranar Laraba, mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Kgalema Motlanthe ya baiyana cewa, kasar tana karkatowa zuwa kasashen Afirka don samo man fetur, bayan katse shigowa da mai daga kasar Iran.

Yayin da Motlanthe ke amsa tambayoyi a majalisar dokokin kasar dangane da batun samar da man fetur a kasar, ya ce, ko da yake har yanzu mafi yawan man da take samowa daga Gabas ta Tsakiya ne, amma a shekarar bara ta samo gangunan mai miliyan 56 daga kasashen Afirka, wato sama da kashi 40 daga cikin dari na yawan man fetur da take shigowa da shi kasar.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, kashi 23 daga cikin dari na man ana kawowa ne daga Najeriya, kana kashi 18 cikin dari daga kasar Angola.

A halin yanzu kuma kasar tana duba shigowa da mai daga kasar Ghana bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a shekarar 2011.

Izuwa yanzu, kasar Afirka ta Kudu ta shigo da mai ganguna miliyan 6.8 daga Ghana, in ji Motlanthe.

A baya kasar Afirka ta Kudu ta kan shigo da mai daga kasar Iran da yawanshi ya kai akalla kashi 26 cikin dari kowane wata. To amma sakamakon matsin lamba daga kasar Amurka, kasar ta rage yawan man da take shigowa da shi daga Iran daga watan Yunin bara.

Dakatar da shigowa da man daga Iran na daga takunkumi da Amurka ta dorawa Iran don hana kasar mallakar makaman nukiliya da ake zargin tana kokarin yi. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China