Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta nuna gamsuwarta kan matakin da hukumar zabe ta musammun (CES) ta kasar Madagascar ta dauka game da takardar jerin sunayen 'yan takarar zaben shugaban kasa na cikin wannan shekara, a cewar wata sanarwa ta kungiyar AU da aka bayar ranar Lahadi.
Shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afrika, Nkosazana Dlamini-Zuma ta nuna jin dadinta game da matakin da hukumar CES ta dauka ranar Asabar kan takardar sunayen 'yan takara na zaben shugaban kasar da zai kawo karshen rikicin siyasa da kuma maido tsarin demokaradiyya a tsibirin Madagascar.
Hakazalika kuma kasar Mauritius ta bukaci kara rubanya kokari daga bangaren kungiyar SADC wajen ganin an warware rikicin kasar Madagascar cikin zaman lafiya. (Maman Ada)