in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi maraba da sunayen 'yan takarar zaben shugaban kasa a Madagascar
2013-08-23 10:39:21 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta bayyana jin dadinta kan fitar da jerin sunayen karshe na 'yan takarar zaben shugaban kasa a Madagascar. A cikin wata sanarwa, kungiyar ta yi kuma kashedi ga 'yan takara na wannan tsibiri dake cikin ruwan tekun Indiya, da su kiyaye duk wani abun da zai gurgunta wannan zabe.

Shugabar kwamitin tarayyar Afrika AU, madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta yabawa hukumar zabe ta musammun ta kasar Madagascar (CES) kan wannan takarda da ta gabatar domin gudanar da wannan zaben shugaban kasa da zai kawo karshen rikicin siyasa, da ya soma tun cikin karshen shakarar 2008, tare kuma da maido da tsarin demokaradiyya a cikin wannan kasa.

Madam Zuma ta bayyana goyon bayan AU kan matakin da CES ta dauka tare da nuna cewa, hukumar ta nuna yin aiki cikin tsanaki da karfafa mutuncinta. Haka kuma ta bayyana gamsuwar AU ga mambobin hukumar CES bisa da jan namijin aikin da suka yi da nauyinsu na girmama kasa mai 'yanci, tare da isar da gaisuwar AU ta musamman ga shugaban wucin gadin kasar Madagascar, Andry Rajoelina bisa ayyukan da ya yi wajen taimakawa kasar a tsawon wannan lokaci na rikon kwarya.

Kuma kungiyar AU za ta cigaba da sanya ido kan kasar, ta yadda za ta rika sanar da kwamitinta na zaman lafiya da tsaro a ko wane lokaci kan cigaban halin ake ciki a wannan kasa domin taimakawa daukar matakan da suka wajaba, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China