in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu za ta bunkasa hadin gwiwa da kungiyar EU
2013-07-10 10:08:59 cri

A ranar Talata, wani babban jami'in gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take ta bunkasa hadin gwiwa da kungiyar kasashen Turai EU don moriyar juna.

Mataimakin ministan dangantakar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ebrahim Ebrahim, yayin wata ganawa da 'yan jarida a Pretoria ya yi nunin cewa, irin wannan hadin gwiwa na zama wata muhimmiyar shimfidar da za ta kara habbaka hadin gwiwa zuwa wani sabon matsayi wato kamar daga tattaunawa kan batun siyasa, zuwa yin hadin gwiwa a fuskar siyasan, kan batutuwa da suka shafi moriyar juna.

Ya ci gaba da cewa, saboda wannan dalili ne kasar Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncin babban taro tsakanin kasar Afirka ta Kudu da kungiyar kasashen Turai SA-EU, wanda za'a yi ranar 18 ga watan Yuli na shekarar nan, in ji Ebrahim.

Ana sa rai cewar, wannan taro mai taken 'samar da aikin yi ta hanyar zuba jarin cikin gida' zai kawo bunkasar hadin gwiwa tsakanin Afirka ta Kudu da kasashen Turai.

Ebrahim ya kara da cewa, makasudin wannan hadin gwiwa tsakanin Afirka ta Kudu da kungiyar kasashen Turai shi ne wajibi ya zamo mai tallafawa muhimman manufofi da shirye-shirye na kasar Afirka ta Kudu a matakin kasa, yanki da kuma Afirka domin kawar da talauci da koma baya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China