Firaministan kasar Syria Wael al-Halqi ya fada a ranar Laraba cewa, 'yan tawayen kasar na gab da wargajewa, yayin da 'yan tawayen da ke samun goyon bayan kasashen yammaci suka nanata bukatarsu na kawar da gwamnatin kasar, a matsayin sharadin taswirar kawo karshen rikicin da aka dade ana fuskanta a kasar.
Kalaman firaministan sun zo a lokacin da kafofin watsa labarai suka bayar da rahoton da ke ayyana nasarar da sojojin gwamnatin kasar suka samu a tsaunin al-Khmais da ke arewacin lardin Latakia a ranar Laraba.
A halin da ake ciki kuma, kamfanin dillancin labarai na kasar Syria, SANA, ya bayar da rahoton cewa, sojojin sun kara samun wata nasara a biranen Homs, Daraa da kuma Aleppo, duk da cewa, mutane 5 sun jikkata a garin Homs lokacin da makamin roka ya fada kan gundumar Ashrafieh.
A jawabinsa, ministan watsa labarai na kasar Syria Omran al-Zoubi ya ce, nasasorin da sojojin gwamnatin kasar ke samu, za ta taimaka wajen samun nasara kan kungiyoyin 'yan ta'addan da ke dauke da makamai a dukkan lardunan kasar.
Gamayyar kungiyoyin 'yan adawar kasar ta Syria dai ta sha gabatar da bukatar kawar da gwamnatin Assad a matsayin sharadin warware rikicin kasar, matakin da a kullum gwamnatin Syria ke watsi da shi, yana mai cewa, kamata ya yi a fara daukar matakan warware rikicin siyasar kasar ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Sai dai masu sharhi na ganin cewa, wannan kiki-kakar tsakanin sassan biyu, ba za ta taimaka wajen cimma tudun dafawa a matsayin sharadin sassantawa da gwamnatin Assad ba.
A ranar Talata, ministan watsa labaran kasar ta Syria ya fito ya bayyana cewa, yayin da 'yan kasar Syria ke da niyyar warware matsalar siyasar kasar tare da kare iko da martaba kasarsu, sai kuma ga shi a bangare guda, 'yan adawa na wargaza wannan shiri, yayin da kasar Syria ke kokarin yakar 'yan adawa masu dauke da makamai dake da alaka da Amurka da Isra'ila.
Ya ce, 'yan Syria ba za su taba amincewa da duk wani shirin warware siyasar kasar ba, muddin ba Assad ne ya amince da shi ba, idan aka yi la'akari da cewa, ba za a hada batun warware matsalar siyasa da aikin ta'addanci ba. (Ibrahim)