Shugaban wucin gadin kasar Madagascar dake shirin mika mulki Andry Rajoelina ya yi bayani a daren ranar Talata cewa, ba zai zama 'dan takara ba a zaben shugaban kasa dake tafe.
Andry Rajoelina ya bayyana hakan ne a bayanin da ya gabatar ta talibijin, inda ya kara da cewa, zai shirya zabe, sannan ya mika mulki ga wanda ya lashe zaben. Andry Rajoelina ya ce, ya gwammaci ya ajiye burinsa maimakon jefa kasar cikin rikici.(Lami)