Wata hadadiyyar tawagar kungiyar cigaban kasashen kuriyar Afrika ta kungiyar SADC dake karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Mozambique Joachim Chissano ta isa tun ranar Alhamis da yamma a Antananarivo, babban birnin tsibirin Madagascar, domin sa ido kan cigaban da aka samu wajen shirye-shiryen zabubuka a wannan kasa, a cewar wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen kasar da aka fitar a ranar Alhamis. Tun zuwan wannan tawaga, mista Joachim Chissano ya bayyana wa 'yan jarida cewa, wannan ziyara tasa na nauyin kimanta cigaban da aka samu game da shirye-shiryen zabubuka a wannan babban tsibiri, tare jaddada muhimmancin gudanar da zabubuka kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta rikon kwarya CENIT ta tsara.. (Maman Ada)