in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da wakilan nagartattun kungiyoyin likitancin Sin da ke aiki a kasashen ketare
2013-08-16 16:22:56 cri
Shekarar bana ita ce ta cikon shekaru 50 da kasar Sin ta fara aike da kungiyoyin likitanci zuwa kasashen ketare domin samar da taimako wajen kiwon lafiya. Ran 16 ga wata da safe, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasa, kuma shugaban kwamitin kula da harkokin sojoji na tsakiya, Xi Jinping ya gana da wakilan nagartattun ma'aikatan kungiyoyin likitanci da ke aiki a kasashen ketare a babban dakin taron jama'a, inda ya taya su murnar samun yabo bisa ga dukkan ayyukan da suka gudanar a madadin kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin da kuma majalisar gudanarwa ta kasar.

Shugaba Xi ya bayar da wani muhimmin rahoto, inda ya bayyana cewa, cikin dogon lokaci, ma'aikatan kungiyoyin likitancin Sin da ke aiki a kasashen ketare sun dauki hakkin da kasa ta rataya musu, ta hanyar gudanar da ayyukansu na harkokin jin kai a duniya, inda suka dukufa wajen ba da taimako ga jama'ar kasashen ketare, ta yadda za'a inganta ayyukan kiwon lafiyar duniya da kuma kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa da kasa.

Ya kuma jadadda cewa, ayyukan da kungiyoyin likitancin Sin ke yi a kasashen ketare na da muhimmanci wajen ci gaban harkokin diflomasiyyar kasa. Shi ya sa, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yi kokari wajen kyautata zaman rayuwar ma'aikatan kungiyoyin da kuma ba da taimako gare su wajen warware matsalolin da suke fuskanta yau da kullum, ta haka, za' a iya kyautata aikin likitanci na kasar Sin a kasashen ketare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China