Mahukuntan kasar Sudan sun saki tsohon babban mai leken asiri na kasar, Gen Salah Abdalla Gosh ranar Laraba, wanda a baya aka yi masa zargin cewa, shi ne ya jagoranci wani yunkurin juyin mulki kan gwamnatin shugaba Omar Al-Bashir, in ji kamfanin dillancin labaran kasar Sudan, SUNA.
Babban mai gabatar da kararraki na kasar Sudan Omar Ahmed Mohammed ya bayyana cewa, hukumar shari'a ta kasar ta tsai da matakin sakin Gen. Gosh bayan lauyan dake kare shi ya mika mata bukatar neman a dakatar da tuhuma da ake masa, in ji kamfanin dillancin labaran.
Wannan mataki na cikin kuduri ne da aka tsayar a kokarin hado kan kasar domin fuskantar kalubale tare, in ji Mohammed, inda kuma ya jadadda cewa, ba wai an tsayar da wannan mataki ba ne saboda rashin cikakken hujja.
To amma Gosh a nasa bangare ya bayyana wa jama'a da suka taru don masa maraba cewa, an sake shi ne saboda rashin cikakken hujja, inda ya kara da cewa, zai ci gaba da zama mamban jami'yyar 'National Congress Party' mai mulki a kasar, kuma zai ci gaba da aikinsa na mamban majalisar kasar. (Lami)