in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sadarwa ta Zawahri ita ce musabbabin rufe ofisoshin jakadancin Amurka
2013-08-06 14:08:46 cri

Kafofin watsa labaran kasar Amurka sun ba da rahoto ranar Litini cewa, matakin da gwamnatin shugaba Obama ta dauka a makon da ya wuce na rufe ofisoshin jakadancin Amurka kusan 24 da kuma ba da gargadi a duk duniya ya biyo bayan jin sigina da aka yi ta sadarwa ne daga shugaban Al-Qaeda, Ayman Zawahri.

Bisa rahoton da aka buga a shafin internet na jaridar 'New York Times' ranar Litinin da rana, an ce, siginar da aka saurara ta sadarwa ce tsakanin Zawahri da Nasser Wuhayshi, shugaban kungiyar Al-Qaeda a Yemen da yankin Larabawa, inda aka gano wata makarkashiya mafi hadari kan Amurka da sauran kasashen yammacin duniya, wato tun bayan rana ta 11 ga watan Satumban shekara ta 2001. Rahoton ya nuna cewa, an samo wannan bayani ne daga jami'an leken asiri da 'yan majalisa.

An ba da rahoton cewa, Zawahiri ya umarci Wuhayshi da ya kai hari tun ranar Lahadi da ta wuce, to amma ba'a tabbatar da a ina ne ko kuma su waye za'a kaiwa harin ba.

Rahoton ya ci gaba da cewa, ba'a saba ganin shugabannin Al-Qaeda a Pakistan suna tattaunawa kan harkokinsu da kungiyoyin dake da alaka da su ba, don haka bayan da aka jiyo da kuma daukar siginar sadarwa tsakanin shugabannin Al-Qaeda guda biyu, aka kuma tantance, sai ya zama wajibi a dauki mataki, kana aka yiwa 'yan majalisa bayani kan wannan lamari. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China