A gun cikakken zaman farko na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka gudanar a ranar 15 ga wata da safe, an zabi Xi Jinping a matsayin sabon babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar, kana an zabi sabbin zaunannun wakilan hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya, wadanda suka hada da Xi Jinping, Li Keqiang, Zhang Dejiang, Yu Zhengsheng, Liu Yunshan, Wang Qishan da kuma Zhang Gaoli.
A gun taron, an tsaida kudurin nada Xi Jinping a matsayin shugaban kwamitin aikin soja na jam'iyyar, kana Fan Changlong da Xu Qiliang su zama mataimakansa.
Ban da wannan kuma, an zartas da jerin sunayen babban sakatare, mataimakin sakataren, zaunannun wakilai na kwamitin ladabtarwa da aka gudanar da zabensu a taron farko na kwamitin, kuma Wang Qishan ya zama babban sakataren kwamitin ladabtarwa a wannan karo. (Zainab)