Mista Xi ya ce, ya kamata hukumomin dokokin shari'a na kasar Sin su tafiyar da ayyukansu daidai bisa fatan da al'ummar kasar ke nunawa a fannonin shimfida zaman lafiya, nuna adalci, kiyaye hakkoki da sauransu, a kokarin raya kasar Sin mai son zaman lafiya, kana mai bin doka da oda.
Bugu da kari kuma, Xi Jinping ya bukaci a zurfafa sauye-sauye ga tsarin dokokin shari'a, da kin amincewa da duk wata shari'a da ba adalci a ciki, da kuma yaki da cin hanci da rashawa a fannin dokokin shari'a.
Hakazalika, Mista Xi ya jaddada cewa, ya kamata hukumomin shari'a su yi kokarin gamsar da al'umma game da duk wata shari'ar da suka yi, ta yadda jama'a za su iya ganin adalci da daidaici a ciki.(Murtala)