Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya mika gaisuwar bukukuwan bazara na bana dake tafe, da za'a yi ranar Lahadi ga masu aikin gine-gine, masu sharar tituna, jami'an 'yan sanda, da kuma direbobin taksi.
Har ila yau, Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kai ziyara ga wadanda suke ci gaba da yin ayyuka a lokacin bukukuwan sabuwar shekara ta Sinawa.(Lami)