in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin siyasar kasar Sin yana koyar da darussa ga Afirka
2013-04-28 09:51:07 cri

Wani masani 'dan kasar Kenya kuma shugaban cibiyar koyar da tsarin demokiradiya da shugabanci a Afirka(IDEA) Denise Kodhe ya bayyana cewa, kamata ya yi Afirka ta ci gajiyar kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninta da Sin wajen nazarin tsarin siyasar kasar ta Sin, kana ta fito da darussan da zai taimaka mata wajen tsara nata tsarin na siyasa da zai kunshi yadda za a bunkasa tattalin arziki da hada kan kabilu.

Denise Kodhe ya bayyana cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua a Nairobi, babban birnin kasar ta Kenya cewa, tsarin demokiradiya irin na yammaci da Afirka ta ara ba ya aiki a nahiyar, domin bai kawo karshen zaman zullumi da ke tsakanin kalibu ba, sannan ko da kasashen nahiyar da ake ganin suna da tsarin demokirdiya da ci gaban tattalin arziki, bai yi dai-dai da ci gaban da suka samu ba.

Kodhe ya ce, "A halin yanzu, babu wani yunkurin da ake na inganta tsarin siyasar Afirka, duk da bukatar da ake da ita na yin hakan."

Ya ce, kamata ya yi Afirka ta yi koyi da tsarin siyasar kasar Sin da ya tabbatar da mika mulki cikin nasara, kana ya baiwa kasar damar kasancewa kasa mafi karfin tattailin arziki a duniya wadda ta inganta rayuwar al'ummarta. Sannan akwai shaidun da ke nuna cewa, akwai kyakkyawan shugabanci a kasar Sin.

An fara amfani da tsarin demokiradiya irin na yammaci a nahiyar Afirka ne tun farkon shekarun 1990, lokacin da kasashen yammaci suka bayar da tallafin kudi da goyon baya ga 'yan adawa domin su nemi kafa gwamnati mai jam'iyyu da dama, tsarin da galibin kasashen ke aiwatarwa a yau.

Amma duk da irin ci gaban siyasar da ake gain, an samu a nahiyar, har yanzu ana ci gaba da fuskantar rikice-rikice sakamakon bambancin siyasa da kabilanci, lamarin da ke kawo koma bayan ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Kodhe ya bayar da shawarar cewa, tsarin siyasa na kasar Sin zai samar da darussa ga Afirka, har ma shugabanin karkashin laimar kungiyar AU za su iya amfani da wasu daga cikinsu wajen tsara tsarin siyasar kungiyar.

Ya ce, ba wai yana nufin a kwaikwayi tsarin siyasar kasar Sin baki daya ba a Afirka, amma akwai bukatar mu yi koyi daga kasashen Turai, Japan, Malaysia, kana mu koyi darussa masu kyau daga ciki, sannan mu yi amfani da su a nahiyar.

Tun ba yau ba shugabannin a sassa dabam-dabam na nahiyar, ciki har da masana da 'yan kasa ke yin kiran a inganta tsarin siyasar Afirka, amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba.

Kodhe ya ce, tsarin siyasar kasashen yammaci, tsari ne na Turawan mulkin mallaka da bai yi wani tasiri ba a Afirka, don haka akwai bukatar a canja wannan tsari, yana mai cewa, kamata ya yi mu samu kafar hada kan al'adunmu, musamman a cikin tsarin siyasarmu.

A halin yanzu dai, Kodhe yana nazari ne kan tsarin siyasar kasar Sin da nufin bayar da gudummawa ga ajandar yadda Afirka za ta inganta tsarinta na siyasa.

A fili yake cewa, ana ganin yadda darussan tsarin siyasar Sin ke tasiri ga Afirka a matsayin manufar moriyar juna da nahiyar za ta amfana da shi daga kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu, baya ga yadda za ta kara hanyoyin fitar da kayayyakinta zuwa kasar ta Sin.

Amma masana a baya sun lura da cewa, wasu rukunonin shugabannin a Afirka ba su ganin irin fa'idar manufar moriyar juna da Sin, maimakon haka, suna kallon Sin a matsayin wata dama ta dabam ga matsalar dangantakar da nahiyar da samu da kasashen yamma.

Masana sun bayar da shawarar cewa, akwai bukatar samun tsarin siyasar da zai warware matsalar kananan kabilu tare da rungumar su cikin harkokin shugabancin kasa, ta yadda za a kaucewa abkuwar rikice-rikice.

Bugu da kari, masanan sun bayyana cewa, wajibi ne tsarin siyasar Afirka ya iya tafiyar da masana'antu don ci gaban tattalin arziki, ta yadda za a inganta rayuwar 'yan Afirka.

Daga karshe, Kodhe ya ce, kamata ya yi tsarin ya koyawa 'yan Afirka yadda za su iya kama kifi, ba wai su jira a ba su kifi ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China