in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya kara wa'adin dakarun MDD da ke Liberia zuwa wata shekara
2012-09-18 09:51:20 cri

A ranar Litinin ne kwamitin sulhu na MDD ya kara wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiya da ke Liberia zuwa wata shekara.

A wani kudurin da kwamitin ya amince baki daya, mambobin kwamitin mai wakilai 15, sun kara wa'adin tawagar MDD da ke Liberia(UNMIL) zuwa ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2013, bisa la'akari da cewa, "Yanayin da ake ciki a Liberia na ci gaba da haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya."

Kwamitin ya yanke shawarar cewa, muhimmin aikin tawagar ta UNMIL shi ne ci gaba da taimakawa kokarin gwamnatin Liberia na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da kare rayukan fararen hula.

Bugu da kari, kwamitin ya umarci babban sakataren MDD da ya aiwatar da kashin farko na shirin rage sojojin da ke tawagar da yawansu ya kai dakaru 1,990 tsakanin watan Oktoban shekarar 2012 da kuma watan Satumban shekarar 2013.

Sannan za a kara yawan rundunar 'yan sanda a Liberia daga sassa 7 zuwa 10. Karin sassa guda ukun zai kai ga karin jami'ai guda 420.

A shekara ta 2003 ne aka kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta UNMIL don ganin an tsagaita bude wuta bayan yakin basasan kasar da aka halaka kusan 'yan Liberia 150,000 galibinsu fararen hula, kana aka tilastawa wasu da yawansu ya kai 850,000 kaura zuwa kasashe makwabta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China