Gwamnatin kasar Liberia ta musanta zargin da wani rahoton kwamitin binciken MDD ya bayar, wanda ke zargin kasar da samar da mafaka ga sansanin horarwa ta 'yan tawaye.
Yayin jawabi ga 'yan jarida a Monrovia, babban birnin kasar ta Liberia, wanda ministan watsa labaran kasar, Lewis Brown ya saba yi mako-mako, ministan ya ba da tabbaci ga kasashe dake makwabtaka da Liberian cewa, ba za'a yi amfani da wani yankin kasar Liberia ba don gurguntar da su.
Ya ce, Liberia ta fi mai da hankali kan kyautata rayuwar jama'ar kasarta, fiye da shiga wata harka da za ta yi kafar ungulu wa kyawawan tanadi da take nufin samarwa jama'ar kasar.
Ministan ya ba da misali da yawon sintiri da dakarun Liberian ke yi a kan iyakar kasar da Cote d'Ivoire har ma da tisa keyar 'yan tawaye da kuma wadanda aka cafke, a matsayin wani bangaren dagewarta a fuskar bunkasa zaman lafiya da tsaro har ma da kyakyawan zamantakewar makwabtaka a yankin.
'Yan tawaye dake yakar shugaba Alassane Ouattara sun yi amfani da kan iyakokin kasashen Liberia da Cote d'Ivoire wajen kai hare-hare da dama, inda suka kashe mutane 50, ciki har da masu aikin kiyaye zaman lafiyan 'yan Nijar su 7.(Lami)