in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu fasahar aikin hannu na yammacin Afrika na neman kasuwanni
2013-07-08 10:58:39 cri

Shugaban gungun kungyoyin masu fasahar aikin hannu na kasashen gamayyar tattalin arzikin yammacin Afrika (RAEC) Lacina Toue ya yi kira a ranar Lahadi a birnin Abidjan da a samar da kasuwanni a cikin wannan shiyya.

Mista Toue dake magana a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a wannan fanni, ya bayyana muhimmancin kara nemo wasu kasuwannin kayayyakin fasahar hannu da za su taimakawa masu wannan aiki dake shiyyar su kara samun kudin shiga.

Fasahar aikin hannu a wannan lokaci na daga cikin manyan ayyukan cigaban tattalin arziki da na jama'a bisa karfinsa na samar wa al'ummomi zaman rayuwa mai kyau da wadata, musammun ma da biya musu bukatunsu na yau da kullum, in ji mista Toure.

Shugaban RAEC ya kuma bukaci masu aikin fasahar hannu dake kasar Cote d'Ivoire da su hada karfinsu domin fitar da wannan bangaren aiki daga cikin duhu da kuma yin amfani da duk wasu hanyoyi domin fuskantar kalubalolin zamani. Fasahar aikin hannu a kasar Cote d'Ivoire na kunshe da ayyuka daban daban da miliyoyin mutane suke yi.

Bunkasa wannan fanni ya kasance wani babban aiki na hukumomin kasa da shugabannin wannan sana'a.

A lokaci da dama, sun gabatar da ayyukan hadin gwiwa domin daidaita wannan sana'a a matsayin wata dabarar yaki da zaman kashe wando.

A cewar wasu alkaluma na hukumar kididdiga ta kasar, bangaren fasahar aikin hannu ta taimaka wa da kashi 12 na GDP, kana mutane fiye da kashi daya cikin hudu na rungumar wannan sana'a a kasar Cote d'Ivoire. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China