Kungiyar kasashen kudu maso gabashin Afirka COMESA, kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC da kungiyar cigaban kasashen kudancin Afirka SADC na gudanar da wani taro tun ranar Laraba kan harkokin kasuwanci da masana'antu a tsibirin Maurice. Haduwar ta bangarorin uku ta biyo bayan wani taro na manyan jami'ai da kwararru da ya gudana daga ranar 8 zuwa 9 ga watan Yuli. Wakilai kimanin 250 da suka fito daga kasashe 26 suka halarci wadannan taruruka. Kwamitin bangarorin uku ya daidaita yanayin kasuwancin COMESA, EAC da SADC ta hanyar bude wani yanki na musanya cikin 'yanci da aka fadada tare da wata kasuwa mafi girma da wani dandalin tattalin arziki guda domin kara janyo yawan zuba jari da kuma taimakawa wajen bunkasa aikin sarrafawa a matsayin koli. Taron bangarorin karo na biyu da ya gudana a kasar Afrika ta Kudu a cikin watan Yuni na shekarar 2011 ya taimaka wajen amincewa da hanyar samun cigaba bisa la'akari da manufar shirin dunkulewar bangarorin uku. Manufar shirin dunkulewa tana dogaro manyan batutuwa uku wadanda suka hada da dunkulewar kasuwa bisa tushen yankin musanya cikin yanci na bangarorin uku, bunkasa gine-gine domin kyautata yin takara da rage kashe kudi wajen yin wata harkar kasuwanci da kuma bunkasa kamfanoni, ta yadda za'a samun karfin sarrafawa.
Taron kwamitin ministoci na bangarori uku na Maurice a karkashin jagorancin kasar Mozambique, zai kasance wata babbar dama ga kasashe mambobi na duba cigaban da aka cimma ta fuskar shawarwari da kuma shirya dandalin bangarorin uku da taron kwamitin bangarorin uku da aka tsai da shiryawa a kasar Masar wannan shekara. (Maman Ada)