in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maurice na jiran samun bunkasuwar tattalin arziki daga kashi 4 cikin 100 a shekarar 2013
2012-11-12 11:09:26 cri

Gwamnatin Maurice ta bayyana cewa, kasar za ta samu bunkasuwar tattalin arziki da kashi hudu cikin kashi dari a shekarar 2013 bisa ga na wannan shekara dake kashi 3.4 cikin 100.

Kasafin kudin shekarar 2013 da ministan kudin Maurice Xavier-Luc Duval ya gabatar wa majalisar dokokin kasar a makon da ya gabata, na hasashen dala biliyan 2.78 da kasar za ta samu, inda a cikinsu dala biliyan 2.37 a matsayin kudin haraji, lamarin dake bayyana karuwa ta kashi 12.5 cikin 100 idan aka kwatanta da ta shekarar 2012.

Haraji bisa kadarori da ba da hidima sun kasance muhimman fannonin samun kudin haraji tare da hasashe na dalar Amurka biliyan 1.576, inda a cikin dala miliyan 910 za su fito daga harajin da ake bugawa kayayyaki (TVA).

A game da batun kashe-kashen kudi, gwamnatin kasar tana hasashen jimillar dala biliyan 3.06 daga cikinsu dala miliyan 390 za su shafi kashe-kashen kudin cigaba na kai tsaye. A cewar ministan kudin kasar, gibin kasafin kudi, za'a rike shi zuwa kasa, dake kashi 2.2 cikin kasa na arzikin da kasar take sarrafawa, adadin ake ganin mafi kankancin da aka samu a wannan karni na baya bayan nan.

Hakazalika mista Xavier-Luc Duval ya jaddada dalilin da ya sa aka rike adadin rashin aikin yi zuwa kashi 8 cikin 100 a yayin da hauhawar farashin kayayyaki ta ragu da kashi 4.1 cikin 100. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China