Majalisar dokokin kasar Maurice ta amince a ranar Talata da tsarin doka dake ba da dama ga zubar da ciki bisa sharuda hudu. Tsarin dokar ya samu shiga da kuri'u 50 na amincewa da kuri'u 14 na rashin amincewa, manufar ita ce sanya wannan doka cikin kundin hukunta laifuffuka. Ita dai wannan doka za ta ba da dama wajen dakatar da ciki tare bisa son rai (IVG) tare da la'akari da sharuda hudu wadanda suka kunshi cewa idan rayuwar mace na cikin danja har ta cigaba da rike ciki, idan kuma cikin zai janyo wani rauni ko da yaushe ko kuma wata matsala da ta shafi kwakwalwar mace, idan kuma yaron dake ciki na fuskantar hadarin nakasa, macen da ta samu ciki daga dan uwan jininta ko kuma aka ma fyade, haka ma yarinyar da shekarunta na haihuwa ba su wuce shekaru goma sha shida ba. (Maman Ada)