Kwamitin siyasar kudi (CPM) na bankin Maurice ya dauki niyyar rike darajar kudin musanya zuwa 4,90 Repo bisa kashi 100 ga shekara, a yayin wani zaman taro na ranar Litinin, a cikin wata sanarwar da aka fitar a wannan rana da yamma.
CPM ya nuna cewa tun lokacin taron watan Maris na shekarar 2012, hagen tattalin arzikin duniya ya kara ja da baya, a yayin da kuma ricikin kudi a kasashen yankin Euro ke kara tsananta.
Makomar bunkasuwa a yankin Euro da kasar Ingila na nuna wani ma'aunin dake sabawa juna a shekarar 2012, har ila yau kuma makomar tattalin arzikin a Amurka da ta kasashe masu tasowa na samun tangarda.
A wani jefi kuma, matsin lambar hauhawar farashi a duniya sun cigaba da kwantawa, kuma a cikin lokacin farashin kayayyakin bukatun gaggawa sun yi kasa.
A kasar Maurice, yunkurin bunkasuwa zai kasance mai kyau, madaidaici a yayin da kuma tattalin arzikin kasar ke cikin karo da matsalolin da suke da nasaba da rikicin Euro musammun ma a bangaren fitar da kayayaykin kwamitin CPM na babban bankin. ( Maman Ada)