in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma yarjejeniyoyi da dama tsakanin Sin da Nijeriya
2013-07-11 10:00:57 cri

A ranar 10 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na tarayyar Nijeriya, Goodluck Jonathan, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar ta Sin, ganarwar da aka dauka a matsayin ganawa tsakanin kasar da ta fi yawan al'umma a duniya, da kuma wadda ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka. A ganawar da suka yi ta tsawon sa'a guda, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra'ayi dangane da yadda za a dada bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen nasu, da ma kasashen Afirka baki daya, inda suka jaddada muhimmancin taimakon juna, da samun ci gaban tare a matsayin burin bai-daya na kasashen biyu.

Domin maraba da zuwan shugaba Jonathan, shugaba Xi Jinping ya shirya kasaitaccen biki a babban dakin taron jama'a, inda bayan da aka buga taken kasashen biyu, shugaba Xi Jinping ya raka shugaba Jonathan kallon faretin girmamawa.

Yayin shawarwarin da suka gudanar, a madadin gwamnatin kasar Sin da kuma jama'arta, Mr.Xi Jinping ya yi lale marhabin da zuwan shugaba Jonathan, inda a nasa bangaren shugaba Jonathan ya gabatarwa shugaba Xi Jinping ministocinsa sama da 10, da suka rako shi, sa'an nan ya ce, "Kimanin shekaru sama da 10 da suka wuce, na taba kawo ziyara nan kasar Sin a matsayin mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, kuma na yi farin ciki matuka da samun damar sake kawo ziyara a wannan karo, ina godiya gare ka da ma gwamnatin kasar Sin, da kuma jama'ar kasar duka kan yadda kuke karbar mu hannu biyu biyu."

Shugaba Xi Jinping a nasa bangaren ya ce, Sinawa kan ce bako a zuwa na farko ya kan zama amini a ziyara ta biyu, kuma ya yi fatan ta wannan ziyara, shugaba Jonathan zai kara fahimtar kasar Sin, tare da kara ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen biyu gaba, ya ce, "A yanzu haka Sin da Nijeriya kowacensu na dukufa kan gaggauta bunkasuwarta, don haka neman ci gaban kasa ya zama aiki daya da ya hada kanmu,tamkar tsintsiya madaurinki daya, na yi farin ciki da samun damar yin musayar ra'ayi tare da takwarana na Nijeriya, kan huldar da ke tsakanin kasashen biyu, da ma sauran batutuwan da ke jawo hankalinmu duka, domin shata makomar bunkasar huldar kasashen biyu tare."

A yayin shawarwarin kuma, shugabannin kasashen biyu sun cimma daidaito kan bunkasa huldar aminci tsakanin Sin da Nijeriya, ciki har da kyautata tsarin hadin gwiwa, da kuma inganta hadin gwiwar kasashen biyu ta fuskar samarda ababen more rayuwa, da ciniki, da makamashi, da aikin gona da tsaro da dai sauransu. Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin daidaita batun rashin samun daidaiton ciniki tsakanin kasashen biyu.

Huldar da ke tsakanin Sin da Nijeriya na bunkasa yadda ya kamata, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar jakadanci tsakaninsu a shekarar 1971. Cikin 'yan shekarun baya, kasashen biyu sun cimma kyawawan nasarori ta fannin hadin gwiwar da ke tsakaninsu, inda Nijeriya ta zo ta farko a nahiyar Afirka, wajen samar da yawan kwangilolin aiki ga kamfanonin kasar Sin, sa'an nan, ita ce kasa ta farko a Afirka, da ta sanya kudin kasar Sin a tsarin kudaden waje da take tanada. A nata bangare, kasar Sin ta taimaka wa Nijeriya wajen harba wani tauraron dan Adam na sadarwa da ya kasance na farko a Afirka.

A wannan rana, Sin da Nijeriya sun kuma daddale yarjejeniyoyi da dama, wadanda suka shafi tattalin arziki, da fasaha, da cinikayyar, da al'adu da dai sauransu.

A yayin shawarwarin, shugaba Jonathan ya ce, kasar Sin babbar kawa ce ta Nijeriya, da ma sauran kasashen Afirka da suke ma'amala da ita, kuma Nijeriya na nuna godiya ga kasar Sin, sakamakon goyon bayan da take baiwa kasashen Afirka, tana kuma burin hada kai da kasar Sin domin kara cimma nasarori a nan gaba. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China