in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran ziyarar Goodluck Jonathan a kasar Sin zata inganta huldodin Sin da Najeriya
2013-07-09 11:21:05 cri

Tun daga yau ranar 9 ga wata ne, shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu a nan kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da sabon shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya gana da shugaban Najeriya, kana kuma karo na biyu da Goodluck Jonathan ya kawo ziyara kasar Sin bayan shekaru 13 da suka gabata.

A gabannin ziyarar shugaban Najeriya, wakilinmu Murtala yayi hira da mutane daga bangarori daban-daban na Najeriyar, don jin ta bakinsu dangane da ziyarar Goodluck Jonathan a kasar Sin. Ga rahoton da ya hada mana.

A hira da Murtala ya yi da mataimakin shugaban tarayyar Najeriya, Alhaji Mohammed Namadi Sambo, ya nuna cewa, akwai babbar ma'ana ga ziyarar Goodluck Jonathan a kasar Sin a wannan karo.

Ministan kula da harkokin sufuri na Najeriya Sanata Umar Idris na daya daga cikin jami'an da za su takawa shugaban kasar baya yayin ziyarar tasa a kasar Sin. Da yake magana kan ziyararsu a wannan karo, ya sa ran ziyarar Goodluck Jonathan a kasar Sin zata inganta huldodin Sin da Najeriya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China