A ranar 1 ga watan Agusta, shugaba Jonathan ya rubuta wata wasika domin taya murna ga Musulman Nijeriya na shiga watan Ramadan, wanda yake da muhimmancin gasket ga musulmai.
Jonathan ya ce, a watan Ramadan Allah ya kan amsa addu'o'in Musulmai, sabo da haka ya ce, ya kamata dukkan Musulman Nijeriya su yi amfani da wannan kyakkyawar dama, su yi addu'a ga kasar wajen samun kyakkyawar makoma.
Jonathan ya ci gaba da cewa, yana fatan Musulmai za su hada kai da sauran al'ummar kasar, ta yadda za su iya taimakawa gwamnati wajen samun bunkasuwa.(Danladi)