in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tan 150 na kifi aka zuba a kasuwannin Conakry albarkacin watan Ramadan a Guinee
2012-07-23 14:39:09 cri
Kimanin tan 150 na kifi aka zuba a karshen makon da ya gabata a kasuwannin birnin Conakry, babban birnin kasar Guinee, matakin da zai taimaka wajen kawo sauki ga al'ummar kasar a cikin wannan wata na Ramadan, wanda ya kasance lokacin da ke samun karuwar farashin kayayyakin masarufi. Wadannan tan 150 da kamfanin kamun kifi na kasar Sin (CNFC) ya kawo sun zo daidai da lokacin da ake bukata kuma sun cike matsalar rashin kifi da ake da ita a babban birnin kasar Guinee, kana wannan na cikin tsarin da gwamnatin kasar Guinee ta dauka na samarwa kasuwannin kasar tan 39870 na kifi.

A cikin wannan tsari na gwamnatin kasar, tuni aka zuba tan dubu 25 na kifi a cikin kasuwannin dake birnin Conakry. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China